Yaki da kwararowar hamada a nahiyar Afirka

Babban sakatare na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon
Image caption Majalisar dinkin duniya na kaddamar da shirin yaki da kwararowar hamada a kasashen nahiyar Afirka

A ranar Litinin ne majalisar dinkin duniya ke kaddamar da shirin shekaru goma na kare kasashe masu karancin danshi a duniya daga kwararowar hamada.

Za'a kaddamar da shirin ne a wasu bukukuwa da za'a gudanar a garin Fortaleza na Brazil da kuma Nairobi babban birnin kasar Kenya.

A cewar majalisar dinkin duniyar dai, kwararowar hamada na barazana ga rayukan mutane fiye da biliyan guda da ke zaune a kasashe kimanin dari .

Nahiyar Afirka ita ce ta fi fuskantar barazanar kwararowar hamadar.