Dan sanda ya harbe kansa a Kano

A Nigeria Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani dan sanda mai mukamin saje, Ibrahim Abdullahi, wanda ya harbe kansa bayan da ya harbi babban jami'in 'yan sanda na ofishin 'yan sanda dake garin Dakatsalle a karamar hukumar Bebeji DSP Abdullahi Umar.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake kokarin bincikar saje Ibrahim bisa zarginsa da daukewa wani mai kanti Naira Dubu Hamsin.

Wannan dai shine karo na farko da wani dan sanda a rundunar 'yan sandan ta Kano ya yi irin wannan kundumbala ga kansa da kuma wani abokin aikinsa.