Ambaliyar ruwa na tabarbarar da al'amura a Nijer

Kungiyar bayar da agaji ga kananan yara ta Save the Children ta ce matsananciyar ambaliyar ruwa na haddasa karin tabarbarewar lamura a Nijar inda yara kusan dubuuku ke fuskantar barazana daga gagarumin karancin abinci.

Wata ma'aikaciyar bayar da agaji ta kungiyar wadda ba ta dade da komawa daga Zinder ba,daya daga cikin yankunan da abun ya fi shafa, ta bayyana ganin kasusuwan dabbobin da suka mutu da gidajen da suka fadi da kuma hanyoyi da kayan gonar dake shafe da ruwa.

Ta ce mutane na fuskantar matsala wajen zuwa cibiyoyin kula da lafiya domin samun kulawar da suke bukata.

Mun ga ruwa ya mamaye amfanin gona abinda zai iya haddasa mummunar illa ga girbin badi.

Kasar dai na fadi tashi na jure wa mamalar ruwa daga tunbatsa mafi girma da kogin kwara yayi a cikin shekaru 80 da suka wuce.

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar na fuskantar matsalar yunwa mafi kamari a cikin tarihi.