Haramcin fitar da hatsi daga Rasha na fara aiki

Haramcin fitar da hatsi daga kasar Rasha ya kankama
Image caption Rasha na daya daga cikin manyan kasashen duniya dake samar da alkama

Dokar hana fitar da hatsin daga Rasha wacce daya ce daga cikin manyan kasashen da ke samar da hatsi na duniya na zuwa ne daidai lokacin da farashin hatsin ya yi tashin gwauron zabi bayanda fari ya aukawa Rashan a watan Yuni.

Wannan haramacin na fitarda hatsin zuwa kasashen ketare zai kai har zuwa karshen shekarar da ake ciki.

Mr. Putin yace za'a iya dage haramcin fitarda hatsin harma zuwa cikin shekara mai zuwa yayinda shugaba Dmitri Medvedev yayi hasashen cewar za'a dage haramcin fitarda hatsin kafinma karshen shekarar da ake ciki, ya danganta da yadda aka samu girbi in ji shi.

Amma sai dai a jiya mataimakin Mr Putin yace gwamnati zata yanke shawara a cikin watan oktoba akan ko ta dage haramcin fitarda hatsin ko kuwa a'a.

Bayanai daga ma'aikatar gona ta kasar na nuni da cewar Rasha bama zata samu hatsin da zata ketara dashi zuwa kasashen wajenta ba, tumma daga amfanin gonar wannan shekarar koma da a ce ta dage haramcin kama daga shekara mai zuwa