Petraeus ya ce yana da 'yancin baiwa Obama shawara

Janar David Petraeus
Image caption Janar David Petraeus

Sabon kwamandan dakarun kasashen waje a Afghanistan, Janar David Petraeus, ya ce yana da 'yancin bayar da shawar a game da shirin Shugaba Obama na soma janye dakaru daga shekara mai zuwa.

Janar Petraeus ya ce a cikin 'yan watanni ne a zahiri aka soma samun ci gaba.

Wakilin BBC a Kabul ya ce wannan ne karon farko da wani jami'in Amurka mai girma kamar haka ya bayyana yiwuwar jinkirta yunkurin janye dakarun.

A cikin watan Yuli dakarun da Amurka ke jagoranta sun fuskanci asarar rayuka mafi yawa fiye da duk wani wata tun hambarar da Taliban shekaru tara da suka wuce.