An wallafa littafin daya soki Wen Jiabao na China

Firaministan kasar China Wen Jiabao
Image caption Wani littafi da aka wallafa ya bayyana Firaministan kasar Sin Wen Jiabao a matsayin dan wasan kwaikwayo

Wani dan adawa a kasar China ya kalubalanci mahukuntan kasar da sabon littafinsa da ya kushe kallon da ake yiwa firaminista Wen Jiabao a matsayin mai ra'ayin kawo sauyi.

A yau ne a yankin Hong Kong za'a fara sayar da littafin nan mai suna babban dan wasan kwaikwayon kasar China: Wen Jiabao

Za'a fara saida littafin duk da tsare marubucin Yu Jie da 'yan sanda su ka yi a watan jiya, inda su ka tsawatar da shi game da buga littafin.

Yu Jie ya bayyana cewar da Wen shugaba ne na gari da gaske, kuma mai karfin hali da hangen nesa, da ya yi kokarin kawo sauyin siyasa a China a wannan lokaci mai muhimmanci a tarihinta, amma ba jagoran gaske ba ne don haka bai tabuka komai ba.