Taliban ta jefe wani mutum da wata mata

'Yan Taliban
Image caption 'Yan kungiyar Taliban

Kungiyar Taliban a arewacin kasar Afghanistan ta sa an yi rajamu a kan wani mutum da wata mata, wato ta sa an jefe su har suka mutu, bayan a zarge su da aikata zina.

An jefe mutanen ne a wata kasuwa , a kan idanun mutane kimanin dubu daya.

An zargi mutumin ne wanda ke da aure da alaka da matar, ita kuma wadda aka yi wa baiko.

An kai su wani filin baja koli, inda aka jefe su.

Matar dai ta rasu nan take, amma mutumin bai cika ba.

Sai 'yan Taliban din suka dawo suka harbe shi.

Su dai mayakan sa kan na daukar kansu ne a matsayin cewa sune gwamnati a yankin Kundz.

Karfinsu a can din na sake karuwa, kuma har da kudin haraji suke karba.

Hukumar dake kula da hakkokin bil adama a Afghanistan dai tayi Allah Wadai da wannan kisan, wanda take ganinsa a matsayin rashin tausayin da mayakan sa kan ke dashi.

Duk da dai cewa ba kasafai ake yin irin wadannan kashe kashen ba, sannu a hankali, suna yawaita.

A farkon watan nan ne dai kungiyar Taliban din ta zane wata mai ciki da mijinta ya rasu, sannan daga baya suka kashe ta bisa ga zargin aikata zina.