'Yansanda a jihar Ribas sun kwato wata mata

'Yan gwagwarmayar Niger Delta
Image caption 'Yan gwagwarmayar Niger Delta

A Yammacin ranar lahadi ne , 'yan sanda a Jihar Ribas dake ke Kudu maso Kudancin Najeriya, suka yi sa'ar kwato wata mata da wadansu wanda ake zargin cewa masu garkuwa da jama'a ne suka sace, kusan Wata daya ke nan da ya wuce. A sanarwar da Hukumar 'yan sandan Jihar , wanda Kakakin Hukumar, Dokta Rita Inoma Abbe ta aikewa BBC , ta ce wandansu Mutane su hudu ne sanye da Kayan Sojoji suka dauke Matan mai suna Mrs Fidelia Ireagbu ,a watan da ta gabata a Fatakwal babban birnin jihar Ribas, Dokta Rita Abbe ta kara da cewa, sun sami sa'ar kwato matar ne, a yayin da suka kai mamaya Sansanin wadanda ake zargin cewa suna tsare da ita a kauyen Akwuabo, dake Karamar Hukumar Etche. A lokacin samamen dai, Hukumar 'yan sanda ta shaidawa BBC cewar takame mutane Uku ,ciki har da mai taimakasu da neman Sa'a ( wato mai tsafi).

'Yan sandan harwau sun sami bindigogin harba ruga, guda Hudu da kananan nakiyoyi da kuma adduna da wukake.

Hukumar 'yansandan dai bata ambachi yawan kudin masu garkuwan suka nema ba a yayin da suke tsare da Mrs Fidelia.

Hukumar 'yansandan ta Jihar Ribas , ta ce har yanzu, tana kokarin wajen ganin ta kama Shugaban masu garkuwan Mista Ndudiri Emuka wanda ya fito daga Karamar Hukumar Etche dake Jihar Ribas. Duk dai da cewa Hukumar 'yan sandan Najeriya na ta ikrarin cewa sai ta kawo karshen lamarin garkuwa da Jama'a da ta yi Kamari a Kasar, musamman ma a yankin Kudu maso Kudanci da kuma Gabashin Kasar al'amarin na neman zama ruwan dare. A da dai, da aka fara Sana'ar kamen Turawa da kuma wasu Fararen Fata kawai ake Sace wa, amma daga baya sana'ar ta kai ga hatta ma bakaken Fata 'yan Kasa suma Sace su ake yi, ana garkuwa da su har sai an bada wasu kudaden da masu kamen ke bukata.