Kotu ta dakatar da auren jinsi guda a California

Jahar California dake kasar Amurka
Image caption Kotu ta dakatar da auren jinsi guda a jahar California dake kasar Amurka

Wata kotun daukaka kara ta tarayya a Amurka ta dakatarda auren jinsi guda a jihar California inda ta ce za ta duba ta gani ko haramta auren jinsin da jihar ta yi ya dace da tsarin mulkin kasar.

Makonni biyu da suka wuce dai wata kotun daban ta soke haramcin inda tace ana iya cigaba da daura aure tsakanin jinsi gudan daga Larabar wannan makon.

Amma kotun daukaka karar ta umarci masu bukatar daura auren da su jira zuwa watan Disamba sanda za ta kammala yanke hukuncin.