Rashin sanya hannu akan dokar zabe zai kawo wa INEC cikas

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Image caption INEC tace rashin sa hannun shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan akan sabon kundin dokokin zabe na shekarar 2010 zai janyo mata cikas

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC tace rashin sa hannun shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan akan sabon kundin dokokin zabe na shekarar 2010 zai janyo mata cikas wajen fitar da jadawali da kuma ka'idojin zabe mai zuwa.

Hukumar dai tace yanzu tana zaman jiran sa hannun shugaban kasar ne a kan sabon kundin dokokin kafin ta baiyanawa 'yan Najeriya yadda zabe mai zuwa zai kasance.

A kwanakin nan ne dai majalisun dokokin kasar suka amince da sabon kundin dokokin zaben wato electoral act 2010 a turance, amma kuma a cewar hukumar zaben, sai shugaba Goodluck Jonathan ya rattaba hannunsa akan kundin kafin ta iya fara aiki dashi.

Shi dai kundin ya kunshi sauye-sauye da dama da 'yan majalisun jihohi da na tarayya suka yi ta tafka mahawara kafin amincewa dasu.