Hari a Baghadaza yayi sanadiyar mutuwar mutane 50

Hari a Baghadaza
Image caption Hari a Baghadaza

Jami'an kiwon lafiya a Iraki sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai zuwa wata cibiyar daukar aikin soja, a Bagadaza, babban birnin kasar, yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50.

Haka nan kuma wasu mutane sama da 100 sun samu raunika.

Wani dan kunar bakin wake ne ya shiga cikin cincirindon mutanen dake jira a dauke su aikin sojan inda ya fasa wani bamb.

An kai wannan hari ne yayinda Amurka ke dab da kammala janye sojojinta na bakin daga, duk da yake wasu sojojin dubu hamsin zasu ci gaba da zama a Irakin, domin taimaka dakarun Irakin.

Harin zai kara rura wutar muhawara a kan ko a shirye dakarun tsaro na Iraki su ke su ci gaba da aikin tabbatar da tsaro daga inda Amurkawan suka tsaya.

Jami'an Amurka na cewa duk da irin wadannan hare hare d ake kaiwa, ba zasu sauya shawararsu ta janye sojojin da ke bakin daga ba, domin kuwa a cewarsu har yanzu tash-tashen hankulan da ake fama da su ba su kai na lokacin da ake ganiyar ta da kayar baya ba.