Hukumar WFP ko PAM za ta rage taimako

Masu fama da yunwa a Niger
Image caption Niger

Hukumar bada agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce gibin da aka samu na kudi ya tilasta ma ta dakatar da shirinta na ciyar da wasu iyalai a Nijar wadanda suke da yara kanana 'yan sama da shekaru biyu.

Kungiyar agaji ta OXFAM ta bayyana matakin da cewa yana da matukar tayar da hankali. Kimanin rabin al'umar kasar ta Nijar, wato mutane miliyan takwas ne ke bukatar agaji.

Wani jami'in kungiyar ba da agaji ta Oxfam, Rob Bailey, ya ce yin hakan zai bar mutane da dama ba tare da wani agaji na binci ba:

Ya ce sun kiyasta cewa kusan kashi sittin cikin dari na mutanen da al'amarin ya shafa ba za su samu agaji daga hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ba idan dai har aka dauki wannan mataki.