Bankin duniya zai baiwa Pakistan rancen kudi

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Babban bankin duniya zai baiwa Pakistan rancen dala miliyan dari tara domin sake gina kasar.

Kamar yadda babban bankin duniya yace yawan mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a Pakistan zasu kai mutum miliyan ashirin amma sai dai babban bankin yace ana samun tafiyar hawainiya dangane da irin taimakon da ya kamata ace kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa suna bayarwa.

Jam'ian majalisar dinkin duniya sunce gwamnatocin wasu kasashen basu gamsu da cewar za'a yi amfani da irin kudaden da zasu bayar ba ta hanyar daya dace .

Sun damu da batun cin hanci da rashawa da kuma fargabar cewar maiyiwuwa ma a karkata akalar irin kudaden da zasu bayar zuwa wata hanya ta daban.

Kasar Amurka dai ita ce kasar da ta fi bada gudummuwa mafi tsoka ya zuwa yanzu. Ta bada dala miliyan saba'in da shida. Bayan ita kuma sai kasar Burtaniya.

Babban bankin duniya ya yi alkawarin dala miliyan dari tara kuma za'a yi amfani da kudaden wajen gudanar da manyan ayyuka da kuma sake gine gine a pakistan.

Gwamnatin Pakistan ta kimanta cewar ana bukatar dala biliyan goma sha biyar domin sake gina kasar