An zargi 'yan sandan Najeriya da cin zarafin bil'adama

Yan sandan Najeriya
Image caption An dade ana zargin 'yan sandan Najeriya da cin hanci da rashawa sabawa doka

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi hukumar yan sandan Najeriya da aikata wasu abubuwa da dama da ke barazana ga sha'anin tabbatar da doka da oda a kasar.

A cikin wani rahoto da ta fitar a Lagos, kungiyar mai hedkwata a birnin New York, ta ce cin hanci da rashawa da yayiwa hukumar katutu, ya kan sa a wasu lokutan, 'yan sanda su tsare mutane wadanda basu ci basu sha ba.

Kungiyar ta zargi 'yan sandan da neman kudi a wurin wadanda aka tsare, a yayin da wasu ma akan gana musu azaba, har ma ta kai ga kisa.

Rahoton ya ce ana sanyawa kananan yan sanda ka'idar abinda za su kawo a matsayin hancin da suka karba, domin a samar masu da matsayi mai maiko.

Rahoton ya kara da cewa direbobi a shingayen bincike na 'yan sanda, da 'yan kasuwa, da attajirai da wadanda aka kama, suna daga cikin na gaba gaba a wadanda ake bukatar su bada wani nau'i na hanci.

Image caption 'yan san dan Najeriya na binciken wata mota a kan hanya

Kuma akwai ma lokutan da wasu 'yan sandan ke bindige mutanen da suka ki bada hancin.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki mataki, tare da kaddamar da wani bincike mai zaman kansa domin gano jami'an dake da laifi da nufin hukuntasu.

A yayin da wannan kungiya ta fito da wannan rahoto, wasu na ganin jama'ar kasa ma na kara yawaitar wannan al'amari tsakanin 'yan sandan, inda su kan yi kokarin baiwa 'yan sanda abin da suke kira, na Goro, da zarar sun shiga cikin wata matsala.

Martani

Amma a martanin da ta mayar, rundunar `yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba ta ji dadin rahoton da Kungiyar kare hakkin bil`adaman ta fitar ba, saboda da ganinsa an tsara shi da nufin cimma wata manufa.

Kuma ko kadan bai ba da hoton gaskiyar abin da yake faruwa a tsakanin jami`an `yan sandan kasar ba.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar Mr Emmanuel Ojukwu ya shaidawa BBC, an kara wa rahoton gishiri ne don a cimma wata manufa.

"Kuma rahoton ya kunshe wasu zane-zane da dama da aka yi da nufin kafa hujja wadanda kuma suka harzuka mu. Ba gaskiya ba ne a ce `yan sanda mahara ne ba masu kare jama`a ba," in Ji Ojukwu.

'yaranmu na karbar taro da sisi'

Ya kara da cewa a baya rundanarmu ta janye `yan sanda da ke kula da wasu, amma haka aka yi ta kokawa lallai sai `yan sandan su koma. Da mahara ne ai da ba wanda zai so su kusance shi.

Dangane da zargin almubazzaranci da kungiyar ta yi wa `yan sandan kuwa, kakakin cewa ya yi:

"`Yan sandan Najeriya sun fi kowa fuskantar sa-ido a Najeriya saboda akwai bangarori da dama da ke sa-ido a kanmu, wadanda kuma ba mu da ikon taka musu birki a aikinsu".

"Mun yarda ce akwai wasu matsaloli tattare da jami`anmu ta fuskar karbar taro da sisi daga hannun jama`a da cin hanci da rashawa da kuma tsare jama`a da yi musu kisan ba gaira babu dalili."

Rundunar `yan sandan dai ta ce da wuya na waje ya fahimci abubuwan da ke hana-ruwa-gudu a aikin `yan sanda, amma babbar matsalar ita ce yadda aka yi watsi da su a baya, ba sa samun isasshen kudin gudanarwa da sayen kayan aiki da kuma rashin horar da jami`ansu a kan dabarun aiki irin na zamani.