Kwalara a Bauchi ta hallaka mutane 67

Mai fama da kwalara
Image caption Mai fama da kwalara

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon barkewar cutar kwalara a Jihar Bauchi, ya karu zuwa mutane 67.

Kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Yahaya Jalam, ya shaidawa BBC cewar an samu barkewar cutar, wadda ta kama mutane kamar 1,742 a garin Bauchi da kuma karamar hukumar Ganjuwa.

Kwamishinan kiwon lafiyar ya ce a yanzu haka gwamnati ta bayar da umarnin a yiwa duk wanda ya kamu da wannan cuta magani ba tare da ya biya ko kwabo ba.

Haka nan kuma gwamnati ta kaddamar da wani shiri na wayar da kan jama'a a fadin jihar baki daya domin tabbatar da mutane suna tsaftace muhalli tare da kauracewa shan gurbataccen ruwa.