Kotu ta hana kafa sansanonin sojin Amurka a Colombia

Taswirar kasar Colombia
Image caption Wata kotu a Colombia ta yanke hukuncin cewar kafa sansanonin sojin Amurka a kasar ya sabawa doka

Wata kotu a Colombia ta ce yarjejeniyar da kasar ta kulla da Amurka wacce ta baiwa sojin Amurka damar amfani da sansonin Colombia ta sabawa tsarin mulkin kasar.

Kotun ta ce ya zama wajibi yarjejeniyar ta samu amincewar majalisar dokokin kasar, inda shugaba Santos ke da rinjayen magoya baya kafin ta cika sharadi.

Yarjejeniyar dai ta baiwa dakarun Amurka damar amfani da sansanonin sojin Colombia guda bakwai na tsawon shekaru goma domin kai hari kan fataken miyagun kwayoyi da kuma yan ta'adda.

Wannan hukunci na kotun Colombia zai dadadawa wasu kasashen dake da makwabtaka da kasar Colombian