INEC ta ce Goodluck na kawo cikas ga shirin zabe

Prof Attahiru Jega
Image caption Prof Attahiru Jega

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta jaddada cewa, shirye-shiryen da take yi na gudanar da zabe mai zuwa sun tsaya cik.

A cewar hukumar hakan ya faru ne a sakamakon jinkirin da shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan ke yi wajen sa hannu a kan dokokin zabe, da kuma kwarya-kwaryar kasafin kudin hukumar.

A makon da ya gabata ne dai majalisar dokokin Nigeria ta amince da dokokin zaben da kuma kasafin kudin hukumar, inda yanzu ake jiran sa hannun shugaban kasa.

A cewar INEC, tuni aka makara da sama da makwanni biyu dangane da tsarin da gudanar da zaben, ko da yake ta kara da cewar duk da haka, lokaci bai kure ba.

Tuni dai jam'iyyun siyasa suke bayar da tasu fassarar ga wannan furuci, inda wasu suka fara kiran a dage zaben daga watan Janairu na badi zuwa wani lokaci daban.