Ambaliyar ruwa na dada barna a yankunan arewacin Najeriya

Ambaliyar ruwa a Jigawa
Image caption Ambaliyar ruwa a Jigawa

A Najeriya ana ci gaba da samun ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar, sakamakon ruwan saman da ake shatatawa, wanda kuma ke janyo barna mai yawa.

A yanzu haka kimanin mutane dubu uku, da gidaje sama da dubu biyu ne ambaliyar ta shafa a garuruwa da unguwanni kimanin goma sha biyar, a karamar hukumar Shanono da ke jahar Kano.

Jama'a da dama na zaune a gine-ginen gwamnati, da kuma gidajen 'yan uwa da makwabta.

A makwabciyar karamar hukumar Bagwai ma ambaliyar ruwan ta tilastawa jama'a kauracewa gidajensu.

Irin wannan ambaliyar ruwan ta kuma shafi daruruwan gonaki a kananan hukumomin Wudil, da Ajingi, da Gabasawa da Gaya, inda aka yi asarar amfani mai yawa.

Mutanen da ambaliyar ta shafa na kukan rashin samun agaji daga hukumomi.

A makwabciyar jihar Jigawa ma, ruwan ya mamaye wasu garuruwa a karamar hukumar Ringim, inda ya raba dubban jama'a da muhallinsu, tare da mamaye gonaki.

Ana ganin dai ambaliyar ta faru ne sakamakon tumbatsar madatsar ruwa ta Challawa dake Kano.

A yanzu haka dai galibin al'ummar garin Yakasawa dake Karamar hukumar ta Ringim inda ambaliyar tafi muni, sun kaurace wa garin.