An sami rabin taimakon da ake nema a Pakistan-Inji Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a halin yanzu an yi alkawarin bayar da fiye da rabin abinda ta shata na dala miliyan dari hudu da sittin domin wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Pakistan.

To amma kungiyoyin bayar da agaji dake a kasa sun yi gargadin cewar har yanzu matsalar na cigaba da gudana, tare da munanar yanayi a wasu yankunan haka bagatatan, abinda kuma ke tilastawa karin dubun dubatar mutane tsallake gidajensu.

Miliyoyin mutane ne dai ke bukatar taimakon gaggawa.

Dan siyasar Pakistan, kuma tsohon dan wasan Kurket, Imran Khan, ya kaddamar da nasa asusun neman taimako, yana mai cewar kasar ba za ta iya ci gaba da dogara a kan kasashen duniya ba.

Ya ce, har ya zuwa wannan lokaci muna kallon waje ne.

Alamun da aka bayar sune cewar zamu taimakawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa ne kawai idan dinbim daloli sun zo daga waje.

A halin yanzu dai tana kara bayyana cewar wannan wani tunanin karya ne. Babu wasu daloli dake zowa daga waje.