Palasdinawa da Israela za su fara tattaunawa kai tsaye

Ma'aikatan agaji dauke da wani Bafalasdine da harin Israela ya jikkata
Image caption Ma'aikatan agaji dauke da wani Bafalasdine da harin Israela ya jikkata

BBC ta samu labarin cewa ma'aikatar harkokin wajen Amurka na shirin sanar da cikakkun bayanai na 'ka'idojin da aka shimfida don gudanar da wata tattaunawar neman sulhu ta gaba da gaba tsakanin Israila da Palasdinawa.

A baya dai Palasdinawa sun dage sai a basu tabbacin kafa kasar Palasdinu a yankunan da Israila ta mamaye tun a shekarar alif dari tara da sittin da bakwai. Sai dai a nata bangaren, Israila ta ce a shirye take ta tattauna gaba da gaba ba tare da shimfida wasu sharudda ba.

Wakilin BBC ya ce Prime Ministan Israila Benyamin Netanyahu ya dage a cikin makwannin da suka gabata cewa a shirye yake ya fara tattaunawa ba tare da wasu sharudda ba, sai dai shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas na bukatar samun tabbaci kafin su zauna da kasar Israila.