OPC sun yi kiran a sako Al-Mustapha

Kudirat Abiola

Kungiyar Yarbawa zalla ta OPC ta kira wani taron manema labarai tana neman a sako major Hamza Almustapha, tsohon dogarin shugaban Naijeriya marigayi janar Sani Abacha.

Kungiyar tare da hadin guiwar, kungiyar Niger Delta Peoples Volunteer Force ta Alhaji Dokubo Asari da kuma kungiyar matasa ta arewancin kasar sun ce, ci gaba da tsare su Almustapha shekara 12 ba tare da wani hukunci ba, tauye hakkin bil'adama ne.

Kungiyar ta OPC karkashin jagorancin Fredrick Fasheun ta ce Najeriya ta kulla yarjejeniyar mutunta hakkin dan adam, sai dai kasar ta gaza mutunta wannan yarjejeniyar a kan al'amarinsu Major Hamza Al-Mustapha.

A don haka kungiyar ta yi kira ga shugaba Goodluck Jonathan da ya sanya baki a al'amarin domin a sako major Hamza Al-Mustapha, Jibrin Bala Yakubu, da James Danbaba da Muhammad Rabo Lawal afuwa.

Ana dai zargin mutanen ne da hannu a kisan uwargidan marigayi Mashood Abiola wato Alhaja Kudirat Abiola a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.