Ruwa na kara toroko a Pakistan

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Makonni uku bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta afka wa Pakistan, ruwan na ci gaba da kara toroko a lardin Sindh na kudancin kasar, da kuma wani bangare na Punjab.

A yanzu haka kashi daya cikin biyar na kasar ruwa ya mamaye shi.

Kwamanda Jawad Ahmad na aiki ne da rundunar mayakan ruwan Pakistan, ya kuma ce mayakan ruwan Pakistan sun kwashe mutane kimanin dubu casa'in daga lardin Sindh.

Yace bayan haka ne za su kawo karshen aikin ceton da suke yi. Sai su maida hankali wajen raba kayan agaji.

A wani tatron gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen Pakistan ya ce nasarar da gwamnati ta samu a yaki da ta'addanci, hannun-agogo na iya komawa baya, idan kasar ba ta samu isasshen agaji ba.

Ana samun karuwar agaji

Hukumomin bada agaji na majalisar dinkin duniya sun ce ana samun karuwa a yawan gudummwar da ake samu don bada agaji ga wadanda ambaliyar ruwan kasar Pakistan ya shafa, sai dai ana bukatar kari domin taimaka wa miliyoyin mutane da suke bukatar abinci, da ruwa da makwanci.

A sanarwar da suka fitar a Geneva, hukumomin agajin sun ce neman taimako na farko da majalisar dinkin duniya ta nema na dala milyan dari hudu da hamsin da tara ta yiwu ya karu.

Har wa yau hukumomin sun yi gargadin cewa rashin jiragen sama masu saukar ungulu na iya haifar da mummunan rashin abinci.

A yayinda hanyoyi da gadoji suka rufta, hanyar kawai da za a bi don taimakawa wadanda ambaliyar ta shafa ita ce ta sama.

Wato a yi amfani da jirage don jefa musu abinci, da sauran kayayyaki.

Sai dai hukumar dake bada agajin abincin ta majalisar Dinkin Duniya na da jiragen helikwafta guda goma ne kawai.

Sannan akwai wadansu guda biyar da ake neman hukumar kula da yanayi ta basu umarnin tashi zuwa kasar ta Pakistan a yau juma'a.

Kuma kakakin hukumar, Emilia Casela ta ce suna kokarin kai agajin ga mutane miliyan shida, kuma zuwa yau sun kai ga mutane miliyan daya da rabi.

Kazakila, hukumonin agaji na majalisar Dinkin Duniya na da kwarin gwiwa kan agajin da kasashe suka yi alkawarin bayarwa.

Zuwa yanzu an samu fiye da kashi hamsin da biyar na kudaden da ake nema.