Sabon gargadin ambaliyar ruwa a Pakistan

Masu barin gidajensu
Image caption Masu barin gidajensu

Mahukunta a kasar Pakistan sun sake yin wani sabon gargadi ga jamaa akan yiwuwar wata sabuwar ambaliyar ruwan bayan da kogin Indus ya cika ya batse.

Dubun dubatar jama'a na kauracewa gidajensu a yankin arewa maso yammacin lardin Sindh, sakamakon wannan hannunka mai sandan da hukumomin suka yi.

Dama dai akwai miliyoyin jama'a wadanda suka tagayyara inda suke neman taimako a sakamakon ambaliyar ruwan.

Kungiyar kula da masu kaura ta duniya ta ce gwamnatin Pakistan da kungiyoyin bayar da agaji ba zasu iya biyan bukatun miliyoyin jama'ar da wannan abu ya shafa ba.

Majalisar Dinkind Duniya ta ce an samu kari a kan jumlar kudin agajin da kasashen duniya suka yi alkawari.

A yanzu dai an yi alkawarin bayar da rabin abinda Majalisar ta ce ta na nema domin bayar da taimakon gaggawa.