Pakistan na fuskantar barazanar wata ambaliyar ruwa

Pakistan na fuskantar sabuwar barazanar ambaliyar ruwa
Image caption Akwai yiwuwar afkuwar sabuwar ambaliyar ruwa a Pakistan, makonni uku bayan aukuwar ambaliyar ruwa mafi muni a tarihin kasar

Akwai yiwuwar afkuwar sabuwar ambaliyar ruwa a Pakistan makonni uku bayan aukuwar bala'in ambaliyar ruwa mafi muni a tarihin kasar.

Sabon gargadin da aka sanar ya tilastawa dubunnan mutane dake lardin Sindh wanda ke arewa maso yammacin kasar tserewa daga gidajensu.

Wannan sabon labarin ya kara dagula halin tsaka mai wuyar da Pakistan ke ciki a yayinda ta ke fuskantar ambaliyar ruwa mafi muni a tarihinta

Majalisar dinkin duniya tace mutane miliyan shida na tsananin bukatar agajin gaggawa ama sai dai da dama har yanzu ba su sami wani taimako ba