Yajin aiki a Africa ta Kudu

Masu yajin aiki a Africa ta Kudu
Image caption Masu yajin aiki a Africa ta Kudu

An rufe makarantu sannan ayuyyukan a wasu asibotocin gwamnati sun tsaya cik a Africa ta kudu, bayan da ma'aikata suka fara wani yajin aiki na sai illa ma sha Allahu.

Ma'aikata fiye da miliyan guda ne suka shiga wannan yajin aiki, bayan da tattaunawarsu da gwamnati ta ci tura akan karin albashi.

Kungiyoyin kwadago na neman a yi musu karin kashi 8.6 cikin 100, yayin da gwamnati ta ce zata kara kashi 7 cikin 100.

Ma'aikatan gwamnati sun yi wani yajin aiki na kwana daya a cikin makon da ya wuce, a lokacin da suka mika bukatunsu ga jami'an gwamnati a Pretoria da Cape Town.