Hukumar SSS a Nijeriya ta kama mutane da mugayen makamai

A Nijeriya hukumar leken asiri ta SSS a jihar Borno, ta gabatarwa manema labarai wasu mutane biyar da ake zargi da shigo da muggan makamai da albarusai daga kasashe makwabta.

Bincike ya nuna cewa, ana shirin kai makaman ne zuwa jahar Filato mai fama da rikicin addini da kabilanci.

Masu fasa-kwabrin makamai da makamantansu sun gane wannan hanya ta jihar Borno, wadda ke makwabtaka da kasashen Nijar da Kamaru da Chadi.