Takaddama kan sa hannu a dokar zaben Najeriya

Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar zabe ta Najeriya ta koka cewa rashin sa hannu a kan sababbin dokokin zabe na kawo tsaiko a ayyukanta

A Najeriya, yayin da hukumar zaben kasar ke kukan cewa rashin sa hannun Shugaba Goodluck Jonathan a kan sababbin dokokin zabe, da kuma kasafin kudin hukumar zaben, sun janyo tsaiko ga ayyukan hukumar, wadansu 'yan siyasa na ganin cewa 'yan majalisun dokokin kasar suna da sauran rawar da za su taka wajen ganin cewa shugaban kasar ya sa hannu akan sauye-sauyen da aka yiwa dokar zaben.

Shugaban jam’iyyar PRP, Alhaji Balarabe Musa, ya shaidawa BBC cewa: “Tilas majalisar kasa [ta] fito fili ta gayawa jama’a abin da ake ciki dangane da tsarin mulkin nan da dokar zabe.

“Kuma jam’iyyun siyasa, ko waccensu ta tashi tsaye ta ga cewa ta fadakar da ‘yan Najeriya…”.

Wasu ‘yan siyasar kuma na ganin cewa lamarin na bukatar sa hannun 'yan kasar ne baki daya.

Sai dai 'yan majalisar dokokin sun ce lokacin sake shigowarsu cikin wannan batu bai yi ba.

A cewar Sanata Ahmad Lawan, “Tsarin mulkin Najeriya ya ba shugaban kasa dama ya duba abin da majalisa ta yi…har kwanaki talatin.

“Maganar nan da muke yi, bai wuce mako daya ko kwanaki goma ba da mikawa shugaban kasa wannan doka da kuma kasafin kudin hukumar zabe.

“Ke nan majalisa bat a da hurumi a cikin wannan yanayi—a cikin wannan lokaci—ta ce shugaban kasa ya ki sa hannu saboda haka za ta yi wani aiki a kai.

“Amma ina so in tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa idan har aka kai kwanaki talatin shugaban kasa bai sa hannu ba, to na tabbata majalisa za ta dauki matakin tabatar da cewa ya zama doka, bangaren zartarwa kuma ya aiwatar”.

Shi kuwa Ministan Yada Labarai, Mista Labaran Maku, cewa ya yi ba haka kawai bangaren zartarwar ya ki sanya hannu a kan dokar zaben da kuma kasafin kudin hukumar zabe ba.

“Wadannan dokokin abubuwa ne wadanda [ke bukatar] dole shugaban kasar ya duba [ya ga] mai suka fada, kuma kafin ya sa hannu sai ya kaiwa Ma’aikatar Shari’a don ta duba ta ba shi shawara a kan abin da ya ke [cikin] wannan doka; in kuma daidai ne zai sa hannu ba matsala; amma dai na tabbatar ba da dadewa ba shugaban kasar zai yi abin da ya kamata ya yi”.

’Yan Najeriya da dama dai za su ganin an hanzarta kawo karshen wannan takaddamar saboda hukumar zaben ta kintsa gudanar da babban zaben kasar na badi.

Karin bayani