Amabliyar ruwa ta yi barna a Kano da Jigawa

Ambaliyar ruwa
Image caption Ambaliyar ruwa

A Najeriya ana cigaba da samun ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar, sakamakon ruwan saman da ake shatatawa, wanda kuma ke janyo barna mai yawa.

A jahar Kano, iyalai sama da dubu guda ne suka rasa gidajensu, kuma gonaki fiye da dari da sittin ruwa ya mamaye a garin Bagwai.

Haka kuma a makwabciyar karamar hukumar Shanono, lamarin yafi kamari, inda wasu mutanen suka nemi mafaka a gine ginen gwamnati.

Irin wannan ambaliyar ruwan ta kuma shafi daruruwan gonaki a kananan hukumomin Wudil, da Ajingi, da Gabasawa da Gaya, inda aka yi asarar amfani mai yawa.

Mutanen da ambaliyar ta shafa na kukan rashin samun agaji daga hukumomi.

Amabliyar ruwan ta kuma malale garin Yakasawa a karamar hukumar Ringim a Jihar Jigawa da ke makwabtaka da Jihar Kano.