Mutane miliyan 4 ne suka rasa muhalli a Pakistan

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan hudu ne dake lardunan Punjab da Singh na kasar Pakistan suka rasa muhallansu sakamakon bala'in ambaliyar ruwan data afku a kudancin kasar.

Kawo yanzu kimanin mutane miliyan takwas ne a fadin kasar ke matukar bukatar taimakon gaggawa, inda kuma a yau ne Majalisar Dinkin Duniya ki shirin gudunar da wani zama na musamman don tattauna matsalar.

Tun da farko dai bankin raya 'kasashen Asiya yayi tayin baiwa kasar Pakistan bashin dala miliyan dubu biyu don taimakawa 'kasar shawo kan matsalolin da ambaliyar ruwan ta haddasa.

A yau ne aka shirya Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, zai yi jawabi ga babban taron Majalisar, akan ziyarar ganewa idon da ya kai Pakistan a makon da ya gabata.

Ana sa ran Mr Ban zai bukaci Kasashen dake cikin majalisar, da su kara taimakawa gidauniyar neman taimakon gaggawar da Majalisar ta kaddamar, wadda kawo yanzu, ba ta samu wani abun kirki ba, idan aka kwatanta da irin gudunmawar da ta samu a wasu bala'o'in da suka faru a baya.