Palasdinawa da Israela za su fara tattaunawa kai tsaye - In ji Clinton

Ma'aikatan agaji dauke da wani Bafalasdine da harin Israela ya jikkata
Image caption Ma'aikatan agaji dauke da wani Bafalasdine da harin Israela ya jikkata

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce bangarorin Israela da Palasdinawa sun amince su koma teburin tattaunawa da juna kai tsaye, a karon farko cikin shekaru ashirin.

An gayyaci Pira Ministan Israela Benjamin Netanyahu da shugaban Palasdinawa domin su je Washinton ran 2 ga watan Satumba domin fara tattaunawar.

Bangarorin biyu sun amince su sanya iyakar shekara daya domin tattaunawar.

A baya dai Palasdinawa sun dage sai a basu tabbacin kafa kasar Palasdinu a yankunan da Israila ta mamaye tun a shekarar alif dari tara da sittin da bakwai. Sai dai a nata bangaren, Israila ta ce a shirye take ta tattauna gaba da gaba ba tare da shimfida wasu sharudda ba.

Wakilin BBC ya ce Prime Ministan Israila Benyamin Netanyahu ya dage a cikin makwannin da suka gabata cewa a shirye yake ya fara tattaunawa ba tare da wasu sharudda ba, sai dai shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas na bukatar samun tabbaci kafin su zauna da kasar Israila.

Batutuwa masu sarkakiya

Sai dai masu aiko da rahotanni na cewa, yiwuwar samun daidaito tsakanin bangarorin biyu na da rauni, domin akwai gagarumin sabani a kan muhimman batutuwan da aka samu rashin jituwa a kansu.

Bangarorin sun hadar da gina matsugunan Yahudawa a yankunan da Israela ta mamaye, matsayin birnin Kudus, kan iyakokin kasar Palasdinu da za a kafa nan gaba, da kuma 'yancin 'yan gudun hijrar Palasdinawa na su koma yankunansu.

Har wa yau an gayyaci shugabannin Masar da Jordan domin su halarci fara tattaunawar a Washington.