Amurka ta gayyaci Isra'ila da Palasdinawa zuwa Washington

Isra'ila da Palasdinawa sun amince su koma shawarwarin sulhu kai tsaye, cikin makonni biyu masu zuwa.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta ce an gayyaci shugabannin bangarorin biyu, zuwa Washington, da nufin cinma yarjejeniyar sulhu mai dorewa cikin shekara guda.

Mark egev shi ne kakakin praminidtan Isra'ila;Ya ce Isra'ila ta yi marhabin da gayyatar da Amurka ta yi na fara shawarwarin sulhu kai tsaye da Palasdinawa, ba tare da sharudda ba.

Ganawa ta karshe tsakaninsu a 2008 ne, amma ana ganin cewa wannan ne karon farko cikin shekaru kusan goma, za a tattauna kan muhimman batutuwan da suka zama kadangarern bakin tulu.

Da yake kwatanta yankin gabas ta tsakiya da yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Ireland ta arewa, wakilin Amurka a yankin gabas ta tsakiyar, George Mitchell, ya ce za a iya daukar lokaci ana tattaunawa, to amma ana bukatar hakuri.