Har yanzu akwai zargi kan sakin Megrahi - Inji wani Sanetan Amurka

Wani gungun 'yan majalisar dattawan Amurka ya ce da walakin, kan sakin da aka yi, shekara guda da ya wuce, ga mutumin da aka samu da laifin tarwatsa jirgin saman Amurka a Lockerbie, a 1988.

An kyale Abdulbasit El-Megrahi ya koma gida Libya ne bisa dalilai na jinkai, bayan da aka ce cutar cancer ta ci karfinsa, kuma ba zai wuce watani uku a raye ba.

A wani taron manema labaru, Sanata Robert Menendez ya ce zai so sanin dalilan da suka sa likitan da ya duba Mr El Megrahi, ya gana da jami'an gwamnatin Libya.

Minista mai kula da yankin Scotland, Alex Salmond ya ce abu ne mai wahalar gaske a tantance ainihin iya tsawon rayuwar mutumin dake dauke da cutar cancer mai kisa.