Ana zaben cike gurbi a Gomben Najeriya

Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar Zabe ta ce ta dauki matasa masu yiwa kasa hidima don tabbatar da cewa ba a tafka magudi ba

A Najeriya a yau ne aka shirya gudanar da zabukan cike gurbi na 'yan majalisar dattawa biyu a Jihar Gombe da ke arewacin kasar, bayan rasuwar wadanda ke kan kujerun kimanin watanni hudu da suka gabata—wato Sanata Tawar Umbi Wada na mazabar Gombe ta Kudu da kuma Sanata Kawu Peto Dukku na mazabar Gombe ta Arewa.

Hukumar Zabe ta Kasa mai Zaman Kanta (INEC) a jihar ta Gombe dai ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da wannan zabe.

Hukumar zaben ta ce ta dauki matasa masu yiwa kasa hidima su gudanar da aikin zabukan, kuma a ko wacce rumfar zabe za a bayyana sakamako domin kaucewa magudi.

Kwamishinan zabe na Jihar ta Gombe, Godfrey Miri, ya bayyana cewa jam’iyyu biyar ne ke takara a mazabar Gombe ta Kudu, yayin da jam’iyyu goma sha uku ke takara a mazabar Gombe ta Arewa.

Ita kuwa rundunar 'yan sanda ta jihar ta ce ta tura 'yan sanda sama da dubu biyar domin tabbatar da doka da oda a yayin gudanar da zaben.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Kamba, ya bayyana cewa za a kai akalla ‘yan sanda biyu ko wacce rumfar zabe, baya ga wadanda za su yi sintiri da kuma wadanda ke zaman jiran ko ta kwana.

Wannan zaben cike gurbin dai wani zakaran gwajin dafi ne ga hukumar zaben ta Najeriya, wacce ke shirye-shiryen tunkarar manyan zabukan kasar nan da ‘yan watanni.

Karin bayani