Ana jiran sakamakon zaben cike gurbi a Gombe

Shugaban hukumar zabe ta INEC
Image caption Hankali ya karkata kan rawar da sabon shugaban hukumar zabe Farfesa Jega zai taka

An kammala kada kuri'a a zaben cike gurbi na 'yan majalisar dattawa biyu a jihar Gombe ta tarayyar Nijeriya .

Zaben ya biyon bayan mutuwar 'yan majalisar dattawa biyu dake kan kujerun ne, watau Sanata Tawar Umbi Wada na mazabar Gombe ta kudu da kuma Kawu Peto Dukku, na mazabar Gombe ta arewa, kimanin watanni hudu da suka wuce.

Wannan zabe dai wani zakaran gwajin dafi ne ga hukumar zabe ta Nijeriya wato INEC wadda ake sa ran za ta gudanar da zabuka a duk fadin kasar nan da 'yan watanni.

Sai dai rahotanni sun nuna cewar matsaloli da dama sun dabaibaye zaben cike gurbin wadanda suka hada da satar akwatunan zabe da kuma rashin kai kayan aiki da wuri ko kuma ma rashinsu sam -sam a wasu wuraren.

Haka nan kuma wani hadarin mota yayi sanadiyar rasuwar wasu jami'an dake sa ido kan zaben.