Iran za ta bude tashar nukiliya a Bushehr

A cikin wata tashar nukiliya ta Iran
Image caption Iran ta ce wannan ci gaba ne a yunkurinta na samawa kanta makamashin nukiliya

Injiniyoyin Iran da na Rasha sun fara zuba mai a cikin tashar nukiliyan Iran ta farko da ke Bushehr wadda ke kudancin kasar.

Gwamnatin Iran din ta ce wannan wani gagarumin ci gaba ne a kokarin kasar na samarwa kanta makamashin nukiliya.

Aikin zuba man dai zai ci gaba har zuwa tsakiyar watan Satumba, kuma tashar nukiliyan za ta fara aiki gadan-gadan ne a watan Oktoba ko Nuwamba.

Kaddamar da tashar ta Bushehr dai na zuwa ne bayan an kwashe shekaru ana jinkiri, da kuma nuna damuwar da kasashen duniya ke yi dangane da shirin Iran na habaka makamashin Uranium.