An loda makamashi a tashar bada wutar lantarki ta nukiliya a Iran

Tashar makamashin nukiliya ta Bushehr
Image caption Tashar makamashin nukiliya ta Bushehr

Injiniyoyi sun fara loda makamashi a tashar bada wutar lantarki ta farko mai aiki da makamashin nukiliya a Iran.

Tashar wadda ke garin Bushehr ana sa ran zata fara samar da wutar lantarki cikin watanni biyu ko uku masu zuwa.

Rasha ce za ta riga samar da makamashin.

Birtaniya dai ta ce ta amince cewa Iran na da 'yancin kafa tashar makamashin nukiliya, domin ayyukan da ba na soja ba.

Sai dai ta ce har yanzu Iran ba ta gamsar da kasashen duniya ba cewa ayyukan da take gudanarwa na inganta karfen Uranium, da kuma na wasu madatsun ruwa tana yi ne domin ayyukan zaman lafiya.