'Yan kasuwa na boye abinci a Nijar

Mata na layin karbar agajin abinci a Nijar
Image caption Hadamammun 'yan kasuwa na tsananta matsalar karancin abinci a Nijar

A 'yan watannin da suka gabata dai, al'ummar kasar Nijar ta yi ta fama da matsaloli wadanda suka hada da rikicin siyasa, da karancin abinci, da kuma ambaliyar ruwa.

Kungiyoyin bayar da agaji sun kiyasta cewa kusan rabin al'ummar kasar ne ke bukatar taimakon gaggawa.

To amma a cewar kungiyar bayar da agaji ta Save the Children, al'amura sun kara tsananta sakamakon boye kayan abinci da 'yan kasuwa ke yi domin cin kazamar riba.

Kungiyar ta Save the Children ta yi gargadin cewa hadamammun 'yan kasuwa na jefa rayukan dubban yara cikin hadari.

A cewar kungiyar bayar da agajin, wadannan 'yan kasuwa na sayen kayan abinci ne a kan farashi mai rahusa da zarar manoma sun girbe su, amma kuma sai su boye abincin har sai ya yi karanci sannan su fito da shi, lokacin da manoman ba su da wani zabi illa su sake sayen abincin da matukar tsada.

Akasarin mutane dai ba su da halin sayen abincin, don haka su kan zauna da yunwa.

Kungiyar ta Save the Children ta ce kusan yara dubu dari uku da talatin ne ke fama da rashin abinci mai gina jiki a Nijar, kuma kungiyoyin bayar da agaji ba za su iya ciyar da su ba.

A farkon wannan makon dai hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce karancin kudi ya tilasta mata takaita taimakon da ta ke bayarwa na abinci ga yara 'yan kasa da shekaru biyu kawai.

Kungiyar ta Save the Children ta ce tana yin wani shiri na taimakawa manoma su taskace kayan abincin da suka noma, sannan a ba su rancen kudin da su yi amfani da shi har zuwa lokacin da farashin zai hauhawa, idan suka sayar da kayan abincin da suka noma a kan farashin mai tsada sai su biya rancen.