Ana zaben cike gurbi a Jihar Gombe ta Najeriya

A Najeriya a yau ake gudanar da zabukan cike gurbi na 'yan majalisar dattawa biyu a jihar Gombe.

Ana gudanar da zaben ne bayan rasuwar wadanda ke kan kujerun kimanin watanni hudu da suka gabata.

Ana kuma gudanar da zaben kusan cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sai dai wasu rahotanni na nuna cewar an samu wasu yan matsaloli a wasu wurare na rashin kayan aiki da kuma zuwan kayan aikin kan lokaci.

Wani hadarin mota ya rutsa da wasu jami'an dake sa ido kan zaben, kuma rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun cemutane biyar sun rasa ransu a hadarin.