Gubar darma ta kashe karin mutane a Zamfara

Mutane akalla takwas ne aka tabbatar sun mutu sakamakon cudanya da gubar darma a kauyen Bagega na Jahar Zamfara.

Babbar jami'ar kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medicins san frontier a jahar Ellen Van Der velden ta shaidawa BBC cewar mace-mace sun auku ne a cikin makonnin baya-bayan nan.

Haka ma wasu rahotannin da baa tabbatar ba sunce mutane akalla uku sun mutu sannan wasu da dama kuma sun samu raunuka bayan da wani ramin hakar zinari ya rufta a kauyen Abare dake jahar ta Zamfara.

A kwanakin baya ma mutane da yawa sun rasa ransa sakamakon mu'amala da gubar darmar a cikin jihar ta Zamfara, akasari kananan yara, abinda ya sa hukumomi suka dauki matakin tone kasar wuce da maye ta da wata.