Australiya: Ana tattauna sabuwar gwamnati

Akwatunan zabe a Australiya
Image caption Babu jam'iyyar da ta yi rinjaye a zaben

An ci gaba da kidaya kuri'u a kasar Australiya bayan zaben da aka gudanar.

Ko da yake babu wata jam'iyya da ta yi rinjaye a zaben, hadin gwiwar jam'iyyun Liberal da National masu ra'ayin mazan jiya ya tserewa jam'iyyar Labour mai mulki da kujeru kalilan.

Yanzu dai ’yan siyasar kasar ta Australiya za su shiga tattaunawa don shata kamannin gwamnatin da za ta jagoranci kasar bayan an kasa samun jam'iyyar da ta yi rinjaye kai tsaye a zabukan na jiya Asabar.

Bayan kidaya akasarin kuri'un da aka kada dai, daga Firayim Minista Julia Gillard har abokin hamayyarta na bangaren masu ra'ayin mazan jiyan, Tony Abbott, babu wanda ya samu kujerun da ya ke bukata don kafa gwamnati.

Yayin da Ms Gillard ta ce babu wanda zai iya bugun kirjin ya lashe zaben, Mista Abbott shaidawa dimbin magoya bayansa ya yi cewa halalcin da jam'iyyar Labour ta ke da shi na mulkin kasar ya saraya.

A yanzu dai salon da gwamnatin mai shigowa za ta dauka zai dogara ne a kan wadansu 'yan majalisa da ba su da jam'iyya da kuma na jam'iyyar ’yan rajin kare muhalli ta Green Party.

Daya daga cikin 'yan majalisar da ba su da jam'iyya, Bob Katter, ya shaidawa gidan talabijin na Australiya mai suna Channel 7 cewa zai mara baya ne ga bangaren da zai fi biyan bukatun al'ummar da suka zabe shi.