Shugaba Campaore ya ce zai tsaya takara

Shugaba Blaise Campaore na Burkina Faso
Image caption Shugaba Blaise Campaore ya ce zai tsaya takara a zaben shugaban kasa

Shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

Tun a farkon watan nan ne dai jam'iyyarsa ta Congress for Democracy and Progress (CDP) ta sanar da cewa shi ne zai zamo dan takararta.

Mista Compaore ne dai ke shugabantar kasar tun shekarar 1987, lokacin da ya kwaci mulki da karfin tuwo.

An kuma zabe shi a karo na farko a shekarar 1991.

Akwai sauran 'yan takara shida da suka nuna aniyarsu ta kalubalantarsa a zaben.