Yan Tijjaniya sun kafsa da Yan Izala a Sabo -Ibadan

Mabiya darikar Tijjaniya da kuma yan kungiyar Izalatul bid'a wa Ikamatus sunnah a Unguwar Sabo-Ibadan sun yi wata taho mu gama da juna.

Wasu mutane dai sun samu raunuka a sakamakon rikicin.

Ya dai samu asali ne bayan wani hukunci da wata kotu a jihar Oyo ta yanke inda ta umarci sassan biyu da su dakatar da amfani da lasifika a masallatansu har nan da shekara daya, don kokarin samun maslahar sabanin dake tsakaninsu.

Kusan shekaru biyu dai kenan bangarorin na jayayya tsakanin su.

Jami'an tsaro dai sun dauki matakan dawo da zaman lafiya a unguwar ta Sabo Ibadan.