Cutar kwalara ta bulla a Jihar Kadunan Najeriya

Wasu masu fama da cutar amai da gudawa a Najeriya
Image caption Cutar amai da gudawa ta bulla a Jihar Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna a arewacin Najeriya na nuna cewa an sami bullar annobar ciwon amai da gudawa a karamar hukumar Birnin Gwari.

Bayanai daga jihar dai na nuna cewa tuni mutane kimanin hudu suka rasu a sanadiyyar cutar da ta bulla a garin Kuyallo na karamar hukumar.

Tuni dai jami'an lafiya daga ma'aikatar lafiya ta jihar, da kuma kungiyoyin bayar da tallafi kamar UNICEF suka hallara a wannan karamar hukuma domin duba yadda za a shawo kan cutar.

Wani jami’in kula da lafiya na karamar hukumar, Aliyu Alhassan, ya bayyanawa BBC cewa annobar ta biyo bayan haduwar ruwan sha da kazanta ne.

“Manoma ne su nan; kuma za ka ga suna tare da dabbobinsu a cikin gidajensu.

“Idan ka shiga gidan za ka ga ga kashin dabbobi, ga wurin girki, ga rijiya, ga masai kusa da rijiya, da sauran irin wadannan abubuwa.

“Kuma ga shi lokacin ruwa ne yanzu; saboda haka duk lokacin da aka yi ruwan sama ka ga zai iya gurbata ruwan da ke cikin wadannan rijiyoyi”, inji jami’in na lafiya.

Ita kuwa kwamishinar lafiya ta Jihar Kaduna, Madam Charity Shekari, shaidawa BBC ta yi cewa gwamnati ta shawo kan al’amarin.

Ta kuma ce: “Wani lokaci in mutane ba sa tsaftace muhallinsu, irin wadannan cututtukan su kan taso.

“To sai a zo a gaya musu su tsaftace muhalli, su tabbatar suna tsafta, kuma kar su sha ruwan da ba su dafa ba”.

Cutar ta kwalara dai tuni ta hallaka mutane da dama a wasu jihohin arewacin Najeriya.