Mahukuntan Nijar sun hana wata zanga zanga a Yamai

A jamhuriyar Nijar a yau hukumomin kasar ne suka haramta wata zanga zangar wani hadin gwiwar kungiyoyin addinin musuluncin kasar .

Kawancen yan uwa Musulman dai ya kudduri anniyar gudanar da wani jerin gwano na lumana akan titunan birnin Yamai domin yin Allah wadai da saka kalmar ‘Raba siyasar kasa da Addini ‘ ko ‘ STATE OF NON RELIGIOUSNESS ‘ da turanci ko kuwa ‘LAICEITE ‘ read LA-YI-SI-TE da harshen Faransanci , da majalisar tuntubar jna ta yi a yan kwanakin nan a wani zama da ta gudanar a kan shata sabon kundin tsarin mulki.

Hukumomin da’irar birnin Yamai dai sun yi wannan hani ne a kan cewar shirya wannan zanga zanga ya saba ma dokar mulkin sojan da kasar ta ke a ciki a halin yanzu.