Masu ruwa da tsaki na taro a Pakistan

Ambaliyar Pakistan
Image caption Ambaliyar dai ta raba miliyoyin mutane da gidajensu

Firayim Ministan Pakistan, Yousuf Raza Gilani, ya kira wani taron gaggawa na jami'an kiwon lafiya, da shugabannin larduna, da kuma kungiyoyin agaji, domin duba yadda za a dakile barazanar yaduwar cututtuka a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.

Hakan dai na zuwa bayan kakkausar sukar da gwamnatin Pakistan din ta sha dangane da yadda ta ke tunkarar matsalar ambaliyar ruwan da ta mamaye kasar.

Wakiliyar BBC a Pakistan, Jill McGivering, tace Wannan mataki na Firayim Ministan wani yunkuri ne na shawo kan al'amarin, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke kara matsin lamba ga gwamnati.

Har yanzu dai al'amura a kasar babu kyaun gani; mutane da dama ba sa samun taimakon da suke bukata, suna kuma fama da rashin muhalli, da karancin abinci, da kuma karancin magunguna, yayin da suke fuskantar yiwuwar barkewar cututtuka.

Gwamnatin kasar ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan wannan bala'in wanda ba a taba ganin irinsa ba, duk kuwa da karancin kudi da kayan aikin da ake bukata don fuskantar matsalar.

Masu suka dai sun zargi gwamnatin da rashin iya aiki da ma nuna halin ko-in-kula wajen fuskantar matsalar.

Wannan dai wata mummunar shaida ce da ka iya bata sunan gwamnatin ta Pakistan wadda da ma ake mata kallon rauni da rashin farin jini.