Dalibai sunyi zanga zangar neman sakin Al Mustapha

Zanga zangar neman sako Al Mustapha
Image caption Zanga zangar neman sako Al Mustapha

A Najeriya wata kungiyar dalibai `yan asalin bangaren arewacin kasar suka yi wani jerin-gwano zuwa ma`aikatar shara`ar kasar domin yin kira ga gwamnati da ta duba yiwuwar sakin tsohon mai tsaron lafiyar tsohon shugaban kasar marigayi janar Sani Abacha.

Daliban wadanda ke ikirarin cewa suna da wakilci daga jihohin arewacin Najeriya goma sha tara da kuma wasu takwarorinsu daga kudancin kasar sun bayyana bukatar shugaban kasar ya yi wa Manjo Almustapha da wasu dake tsare da sunan fursunonin siyasa afuwa kamar yadda gwamnati ta yi wa `yan ta-da-kayar-baya da ke yankin Niger-Delta.

Daliban, wadanda ba su samu damar shiga ma`aikatar shar`ar ba saboda girke kofofinta da aka yi, ba tare da yi musu wata kyakkyawar maraba ba sun kwashe lokaci mai tsawo suna zaman jiran tsammani.

Amma daga bayan sun sami mika sakon dake kunshe da kukansu. Manjo Almustapha da wasu dai ana zarginsu da aikata laifuka ne da suka shafi kitsa kisan kai da kuma aiwatar kisan kan.

Kuma Shara`ar tasu na daga cikin sha`ra`o`in da aka kwashe zamani ana yi ba tare da yanke hukunci ba a Najeriya.

Koda a makon da ya gabata sai da wata kungiyar kabilar Yarbawa ta OPC ta yi kira da a saki manjo Almustaphan.