'Yan majalisar Australia na tattaunawa da shugabar kasar

Shugabar Australia,Julia Gillard
Image caption Shugaba Gillard na neman goyon bayan 'yan majalisa

A kasar Australia,'yan majalisa masu zaman kansu, wadanda alkiblar gwamnatin ta dogara a kansu, sun ce za su tattauna ne a matsayin tsintsiya madaurin ki daya kafin yadda a kafa sabuwar gwamnati.

'Yan majalisun uku wadanda suka fito daga yankuna karkara basu yi fice a baya ba , kafin makomar kasar ta koma hannunsu.

Duk da cewa akwai sauran kuri'un da ba'a gama kirgawa ba, babu jam'iyyar da ta samu rinajyen kafa gwamnati.

Julia Gillard ta sauka a babban birin kasar wato Canberra a jirginta, inda ta ke da fatan cewa lokaci bai yi ba da zata rabu da shi.

Ta tafi kai tsaye zuwa ofishin yan majalisar, inda take neman goyon bayansu don cigaba da mulki.

A yanzu tunda bata samu kuri'u mafi rinjaye ba, ya rage mata amun amicewarsu don kaiwa gaci.

Za ta yi musu alkawuran da za su sa su goya mata baya.

Kuma yawancin kamfe dinta ya ta'allaka ta neman goyon bayan mazabun dake kauyuka