Fargabar ambaliyar ruwa a Ghana

Taswirar Ghana
Image caption Taswirar Ghana

Ana ci gaba da zaman dar dar a sassa daban na arewacin Ghana bayan da kasar Burkina Faso ta bude madatsan ruwanta wato Bagre Dam abinda hukumomin Ghana suke ganin ze haddasa mummunan ambaliyar ruwa a arewacin kasar.

Tun a ranan Juma'a da ta wuce da kasar Burkina Faso ta bude madatsan ruwan ne dai ruwa yake ta kwararowa zuwa cikin wasu manyan kogunan dake arewacin Ghana daga madatsan ruwan. .

Rahotannan dake fitowa daga arewacin kasar dai sunce kogunan da suka hada da White Volta da kuma Black Volta duk sun fara cika sakamakon kwararowan da ruwan yakeyi daga madatsan ruwan ta Burkina Faso. A fira da yayi da manema labarai shugaban hukumar bada agajin gaggawan dake arewacin kasar wato Mr. Patrick Akake ya ce a halin da ake ciki yanzu lamarin bashi da ban tsoro saboda wasu tanade tanaden da sukayi don tunkarar lamarin.

Zaman dar- dar

Ya ce sakamakon kashedin da sukayi musu manoman dake noma kusa da bakin gaban kogunan sun girbe anfanin gonakinsu kuma tuni suka tashi daga wuraren. Mr. Patrick Akake yace wani abin damuwa garesu shine yadda basu da issasun kayan agajin da zasu rarraba ma mutane sama da dubu dari uku(300,000) da ambaliyar ruwan zata shafa. Bayanan da wakilin BBC a Accra ya samu dai sunce wani abinda ze iya sa lamarin yayi kamari shine ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ci gaba da shekawa a yankin arewacin kasar. Sai dai kakakin hukumar bada agajin gaggawar wato Manjo Nicholas Mensah mai ritaya ya ce sun cimma wata yarjejeniya da hukumomin Burkina Faso kan yadda zasuyi taka tsan tsan wajen sako ruwan a yayin da su kuma a nasu bangare zasu dauki matakan rage bannan da ambaliyar ruwan zata haddasa. A cikin shekara ta 2007 da Burkina Faso ta bude madatsan ruwan nata dai mutane sama da dubu dari biyu da hamsin(250,000) ne suka rasa matsugunnansu a arewacin Ghana bancin asaran rayukan da akayi sakamakon abaliyar ruwan da ta biyo baya.

Lamarin ya kuma rutsa da anfani gona da dama, abinda yasa gomnati a wannan lokacin ta bayyana baki dayan arewacin kasar a matsayin inda bala'i ya akba ma.