An mikawa shugaban Najeriya rahoto akan rikicin Plateau

Rikcin jahar Plateau
Image caption Rikicin jahar Plateau

A Najeriya, kwamitin da shugaba Goodluck Jonathan ya kafa domin ba shi shawara a kan rikicin jihar Plateau, ya mika wa shugaban rahoton nasa.

Kwamitin ya gano cewa, rikicin bako-da-dan -kasa shi ne ya yi sanadin barkewar rigingimu a jihar, wadanda suka janyo asarar dubban rayukan jama'a da dimbin dukiya.

Kwamitin binciken ya ba da shawarar cewa, zai yi wuya a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin, muddin ba a hukunta wandanda aka samu da hannu wajen ta da rigingimun ba.