Mace-mace sakamakon yajin aikin ma'aikatan lafiya a Katsina

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, adadin majiyyatan dake mutuwa sakamakon yajin aikin da ma'aikatan lafiya ke yi a jihar Katsina yana dada karuwa.

Rahoton da BBC ta samu ya ce, a daya daga cikin kananan hukumomin jihar guda talatin da hudu, yawan kananan yaran da suka mutu a kwana goma sha biyu na yajin ya kai 20.

Kungiyoyin agaji na addinin Islama a karamar hukumar Mashi dake taimaka wa marasa lafiyar ne suka bayyana adadin. Su ka ce yaran sun tarad da ajalin na su ne, sakamakon wani zazzabi mai zafi da ake kyautata zaton na cizon sauro ne.

Ma'aikatan lafiyar na yajin aikin ne domin neman karin albashi da kuma kyautatuwar yanayin aikinsu.